Majalisar karamar hukumar Garun Mallam a jihar Kano ta bai wa mazauna kasuwar Kwanar Gafan wa’adin kwanaki bakwai su tattara kayansu su bar kasuwar nan da ranar 1 ga watan Janairu, 2025. Wannan umarni ya fito ne daga shugaban karamar hukumar, Barrister Aminu Salisu Kadawa, a yayin kaddamar da shirin sake farfado da tattalin arzikin yankin.
Ya gargadi mazauna kasuwar da su bar wurin kafin wa’adin ya cika, tare da jan kunnen cewa duk wanda aka kama ya karya doka, za a dauki matakin hukunci a kansa. “Nan gaba kadan za mu sanar da ranar da za a sake bude kasuwar bayan an kammala gyare-gyaren da za su mayar da ita ta zamani. Sabuwar kasuwar za ta bai wa 'yan kasuwa damar gudanar da harkokin kasuwanci na zamani, wanda zai hada da kayan gona da sauran nau’ikan kayayyakin more rayuwa domin bunkasa tattalin arzikin yankin,” in ji Barr.
ประเทศไทย ข่าวล่าสุด, ประเทศไทย หัวข้อข่าว
Similar News:คุณยังสามารถอ่านข่าวที่คล้ายกันนี้ซึ่งเรารวบรวมจากแหล่งข่าวอื่น ๆ ได้
แหล่ง: thecableng - 🏆 2. / 80 อ่านเพิ่มเติม »